1. main content
  2. main navigation
  3. extra content
  4. head navigation
  5. search
  6. Choose form 30 Languages

 
 
 

 

 | 09.01.2009 | 07:00 UTC

Mutuwar yar kƙsar waje cikn hare haren Isra'ila a Gaza

Jami'an kiwon lafiya a Gaza sun ce wata mace 'yar ƙasar Ukraine ta mutu a cikin wani hari da Isra'ila ta kai a wannan yanki. Wannan mace na zaman 'yar ƙasar waje ta farko da ta mutu a cikin hare haren da Isra'ila ta shafe kusan makonni biyu tana kaiwa akan yankin na Falisɗinawa. Dr. Maoiya Hassanain na ma'aikatar kiwon lafiya a Gaza ya ce sunan wannan mace Olvera Al-Jarou. Ya ƙara da cewa mijinta wani bafalisɗine ne da ya samu horo na aikin likita a ƙasar Ukraine. Ya ce ɗanta mai shekaru biyu da haifuwa shi kuma ya mutu a cikn harin da Isra'ila ta ka a gabacin birnin Gaza.

Amirka ta ƙaurace wa ƙuri'ar tsgsita buɗe wuta a Gaza

A cikin wani abin dake zama koma baya ga alƙawarin da ta ɗaukar wa ƙasashen larabawa  Amirka ta ƙaurace wa ƙuri'ar amincewa da ƙudurin  tsagaita bu€e wuta a zirin Gaza da komitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya kaɗa a jiya alhamis. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice ta ce Amirka ta janye daga jefa wannan ƙuri'a ne sabo da cewa ta na jiran sakamakon da za a samu a ƙoƙarin shiga tsakani da Masar ke yi don kawo ƙarshen hare haren da Isra'ila ta shafe kwanaki 13 tana kaiwa kan Zirin Gaza, inda falisɗinawa sama da 750 suka rasa rayukansu. Janyewar Amirka daga wannan ƙuri'a zai raunana wannan ƙuduri tare da kuma kawo koma bayan matsin lamba da ake yi wa kawar tata Isra'ila da ta biye wa shawarar da majalisar ɗinkin duniya ta gabatar dake yin kira ga janyewar dakarun Isra'ila ga baki ɗaya daga zirin Gaza. Sauran mambobin komitin 14 sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da wannan ƙuduri.

Hasashen karuwar matsayin rashin guraben aiki a Amirka

A yau ma'aikarar kula da ayyuka a Amirka za ta fid da wani rahoto da ake sa ran cewa zai bayyanar da matsayin rashin guraben aiki da ya munana a watan Disamba da ya wuce. Masana tattalin arziƙi sun yi hasashen cewa ana sa ran bayyanar da ƙaruwar matsayin rashin guraben aiki da kashi shida da ɗigo bakwai daga cikin ɗari a watan Nuwamba zuwa kashi bakwai daga cikin ɗari a watan Disamba. Idan wannan hasahen nasu ya tabbata to kenan za a fuskansci matsayin rashin guraben aiki mafi muni a cikin shekaru 15 da rabi da suka shuɗe. Masana tattalin arziƙin sun nunar da cewa kimanin mutane dubu 550 suka rasa guraben aikinsu a wancan wata. Kenan mutane miliyan biyu da ɗari huɗu da 60 suka rasa guraben aikinsu a shekara ta 2008 da ta gabata.

Hare hare akan 'yan jarida a Sri Lanka

 A sri Lanka kafafen yaɗa labarai na gida da na ƙasa da ƙasa sun yi kira ga ƙasashen duniya da su matsa wa ƙasar lamba bayan kisan da aka yi ma wani ɗan jarida da kuma ƙaruwar hare hare akan kafafen yaɗa labaru masu zaman kansu. Ƙungiyar kare 'yan jarida wato Committe to protect Jourmalists  dake da helkwatanta a birnin New York ta yi kira ga jakadun ƙasashen waje dake Colombo babban birnin Sri Lanka da su matsa wa Shugaba Mahinda Rajapakse lamba domin kawo ƙarshen hare haren da ake kai wa kafafen yaɗa labarai a ƙasarsa. Ƙasar Amirka ita kuma ta ƙara muryarta ga la'antar kisan da wasu mutane da ba a gano ko su wanene ba suka yi wa Lasantha Wickrematunga babban editan jaridar Sunday.

Mutuwar sojojin NATO guda biyu a Afghanistan

A ƙasar Afghanistan wani harin ƙunar baƙin wake da aka aiwatar a kuddacin ƙasar ya rutsa da rayukan sojojin Amirka guda biyu. A jiya alhamis ne aka aiwatar da wannan hari kusa da wata kasuwa dake gundumar Maywand na lardin Kandahar. Wani ɗan sanda ya sanar da kamfanin dillacin labaran Reuters cewar sai da kuma wasu farar hula uku suka rasa rayukansu a cikin wannan hari baya ga farar hula 21 da suka jirkata. A cikin jawabin da ya yi shugaban rundunar NATO Gen. David McKierman ya yi Allah wadai da wannan hari inda yace  hakan na bayyanar da haƙiƙanin taken taken 'yan Taliban da suka yi iƙirarin kai harin.



 
Picture of the Day
ImageOfTheDay

DW-TV EUROPE live

Journal (english) - With In Depth