| 03.12.2008 | 17:00 UTC
Rundunar tsaron EU a kosovo
Bayan wata da watani ana taci ba ta ciba, a ƙarshe dai ranar 9 ga watan da muke ciki Ƙungiyar Tarayya Turai ,za ta aika tawagar jami´an tsaronta, da aka raɗawa suna Eulex a ƙasar Kosovo.
A makond a ya gabata ne ,komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri´ar amincewa da aika wannan runduna da zata ƙunshi jami´antsaro da alƙalai daga ƙasashe dabam-dabam na EU.
Hukumomin Pristina, sun jimma suna nuna adawa ga rundunar, da sukewa kallon cikas ga ´yancin ƙasar Kososvo.
A wartan Februaru na shekara bana, Ƙungiyar Tarayya Turai ,ta yanke shawara aika tawagar jami´an tsaro, kimanin dubu biyu a Kosovo, wanda sannu a hankali za su maye gurbin rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Itama ƙasar Serbiya ta nuna matsanciyar adawa da rundunar EULEX, a jiya talata, dubunan jam´a ,suka shirga zanga-zangar yin Allah wadai da ita.






