| 03.12.2008 | 17:00 UTC
Rikici tsakanin Indiya da Pakistan
Gwamnatin ƙasar Indiya tayi tsaye kan bakanta, a game da zargin Pakistan da hannu a cikin hare- haren da suka rutsa da birnin Bombey makon da ya gabata.
Hukumomin Pakistan, sun jaddada wannan zargi, albarkacin ziyara da sakatariyar harakokin wajen Amurika Condolisa Rice ta kai a birnin New Delhi, da zumar sasanta ɓangarorin biyu.
Indiya tace ta na da cikkakar shaida, mai tabbatar da hannu Pakistan a cikin harin, a game da haka, gwamnatin zata ɗauki matakan riga kafi, kamar yadda Pranab Mukherjee Ministan harakokin wajen ƙasar ya nunar:
"Gwamnatin Indiya ta ɗauri aniyar kare al´ummominta da iyakokinta.
Don cimma wannan buri, zamu yi amfani da dukkan matakan da suka dace, kuma muna kira ga ƙasashen ƙetare su bamu haɗin kai a wannan yaƙi da ´yan ta´ada".
Sakatariyar harakokin wajen Amurika, ta buƙaci Indiya tayi takatsantsan,a game da zargin da take wa Pakistan.






